✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano

Kakakin ya ce da zarar sun kammala bincike za su tura waɗanda ake zargin zuwa kotu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami tare da ƙwato motocin sata guda huɗu, bayan wani samame da suka kai.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu nasarar ne a ranar 10 ga watan Mayu, 2025, inda tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin CSP Rabiu Gidado ta kama wani da ake zargi, Saidu Abubakar, a Jihar Filato.

An same shi da wata mota ƙirar Toyota Corolla samfurin 2016 da aka sace wa wani mazaunin unguwar Naibawa a Kano.

Yayin gudanar da bincike, Abubakar ya amsa cewa yana cikin wata ƙungiyar masu satar motoci da fashi da makami, kuma ya bayyana yadda suke aiwatar da ta’asarsu.

Kiyawa, ya kuma ce a ranar 16 ga watan Mayu, jami’an rundunar sun kama wani Ibrahim Isa a Kano, yana ƙoƙarin sayar da wata mota ƙirar Howo concrete mixer da aka sace a Ƙaramar Hukumar Kazaure a Jihar Jigawa.

Kakakin ya ce dukkanin waɗanda ake zargin na taimaka wa bincike, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.