✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamishina ta nemi a hukunta wanda ake zargi da yi wa ’yar matarsa fyaɗe a Gombe

Yanzu haka dai wanda ake zargin yana hannun 'yan sandan kuma suna gudanar da bincike.

Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Gombe, Asma’u Muhammad Iganus, ta ce gwamnati za ta tabbatar da an yi wa ’yar shekara biyu, Maryam Buba da ake zargin mijin mahaifiyarta, Muhammad Magaji mai shekara 47, da yi mata fyaɗe.

Kwamishiniyar tare da tawagarta sun kai ziyara gidan iyalan yarinyar da ke unguwar Jauro Innayo a Gombe, inda ta tausaya mata tare da ba su kayan tallafi kamar su pampers, sabulai da kuma kuɗi.

Asma’u ta sha alwashin cewa za a bi duk matakan shari’a domin ganin wanda ake zargi ya fuskanci hukunci.

Ta ce gwamnati na mara wa ɓangaren shari’a baya don ganin an samu adalci.

Ta jaddada ya kamata a yi wa wanda ake zargi hukuncin ɗaurin rai da rai matuƙar an same sa da laifi, domin hakan zai zama izina ga masu irin wannan ɗabi’a.

Mahaifiyar yarinyar, Hauwa’u Usman, ta gode wa Kwamishiniyar bisa goyon bayan da ta bayar da kuma addu’a a gare ta.

Ta kuma buƙaci gwamnati ta hukunta mijinta da tsauraran hukunci.

Daga bisani Kwamishiniyar, ta nufi hedikwatar ‘yan sandan Jihar Gombe don ganawa da Kwamishinan ‘yan sanda Bello Yahaya.

Sai dai ba ta same shi ba saboda yana bakin aiki.

Duk da haka, ta bar saƙo masa na gudanar da bincike tare da gurfanar da wanda ake zargi a kotu.

Muhammad Magaji, wanda ake zargi da laifin, yana hannun ’yan sanda kuma suna kan bincike.

Rundunar ’yan sandan ta tabbatar da cewa za a gurfanar da shi a kotu da zarar ta kammala bincike.