Mai shari’a Mohammed Yunusa na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ya soke takarar zababben Gwamnan Jihar Abiya, Alex Otti da daukacin ’yan takarar jam’iyyar LP a jihohin Abiya da Kano.
Kotun ta yanke hukuncin cewa tsayawarsu ta saɓa wa dokar zabe ta 2022 ba.
- An Haifi Jariri Na Farko Ta Hanyar Hada Maniyi A Asibitin ABU
- NAJERIYA A YAU: Yadda Kishi Ya Sa Matar Aure Farka Cikin ’Yar Makwabta
An mika kwafin hukuncin da kotun ta yanke ga manema labarai a ranar Juma’a.
A karar da Mista Ibrahim Haruna Ibrahim ya shigar kan Jam’iyyar LP da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), kotun ta ce jam’iyyar ta mika rajistar mambobinta ga INEC cikin kwanaki 30 kafin ayyana zaben fid-da-gwanin a matsayin bai inganta.
Ya ce jam’iyyar ba ta bi tanade-tanaden dokar zabe ba, don haka ba za a iya cewa tana da dan takara a zabe kuma ba za a iya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ba.
Don haka ya bayyana cewa kuri’un da aka bai wa Alex Otti sun tashi a banza.
Ga kwafin hukuncin da kotun ta yanke: