Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ƙaryata wani rahoto da ke yawo cewa yana shirin shiga sabuwar haɗakar siyasa.
A wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana rahoton a matsayin “karya, ba shi da tushe kuma makircin wasu ‘yan siyasa ne.”
- Riƙaƙƙun ’yan daba da dilolin ƙwaya 31 sun shiga hannu a Kano
- Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace ya kamata ta sani
Ya gargaɗi jama’a da ka da su yarda da irin waɗannan labarai marasa tushe.
“An jawo hankalina kan wani rahoto wanda ke bayyana matsayina a haɗin gwiwar siyasa a Najeriya.
“Ina so na fayyace cewa irin waɗannan rahotannin ƙarya ne, ba su da tushe kuma makircin siyasa ne kawai,” in ji Kwankwaso.
Tsohon ministan tsaron, ya bayyana cewa ya zaɓi ka da ya riƙa yin magana a fili kan wasu abubuwan da ke faruwa a siyasar ƙasar nan, amma zai yi magana a lokacin da ya dace.
“Na daɗe da daina yin sharhi kan abubuwan da ke faruwa a siyasa, kuma zan ci gaba da kaucewa yin haka a halin yanzu,” ya ƙara da cewa.
Kwankwaso ya buƙaci ’yan Najeriya da su dinga dogaro da hanyoyin sadarwarsa a hukumance idan suna son sanin matsayinsa ko ra’ayinsa game da wani abu.
“Dangane da hakan, ina roƙon jama’a da su riƙa duba ko sauraron saƙonni da ke fitowa daga shafukana da sauran hanyoyin sadarwarta kawai,” in ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, har yanzu yana ɗaya daga cikin manyan ’yan siyasar da ake sa ido a kansu kan yiwuwar yin haɗaka da wata tafiya ta siyasa.