Likitoci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya sun kafa tarihin kyankyashe jariri na farko wanda aka samar ta hanyar debowa tare da hada maniyin mace da namiji a Arewacin maso Yammacin Najeriya.
Shugaban ayarin likitocin da suka gudanar da aikin, Farfesa Adebiyi Adesiyun ya ce an haifi jaririn ne a ranar 16 ga watan Mayun wannan shekara da misalin karfe 10.53 na safe.
A cewarsa, jaririn mai nauyin kilogram 3 ya fito da cikakkiyar halitta irin ta kowane jariri da ake haihuwa da lafiya.
Aikin wanda shi ne irin shi na farko da aka gudanar a duk fadin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ya sami gagarumar nasara.
- Jami’an tsaro na izgili ga mutanen da aka kai wa hari —Sarkin Musulmi
- Kwankwaso ne ya fara sayar da kadarorin Gwamnatin Kano —Ganduje
Farfesa Adesiyun ya kara da cewa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello ya shafe kusan shekaru 12 yana wannan kokari, amma matsalar karancin kudi ya yi ta kawo masu tarnaki.
Ya ce ko a wannan karon ma, idan ba don hadin gwiwa da suka yi ba da kuma gagarumin tallafi da shugaban asibitin, Farfesa Hamid Ndigas ya basu ba, to kila da ba a sami wannan nasarar ba.
Likitan ya tabbatar da cewa asibitin na da kwararrun likitoci da kayan aikin gudanar da aikin, amma tsadar aiwatar da aikin ya sa aka kasa samun gudanar da shi tuntuni.
Farfesan ya yi bayanin cewa wannan hanya ce kadai za ta share wa jama’a musamman wadanda ba sa haihuwa hawaye, su samu cikin sauki.
Ya ce yanzu haka ma akwai al’umma da yawa da suke jira, amma rashin ingantaccen dakin gwaje-gwaje na musamman ke kawo tsaiko ga aikin.
Ya shawarci masu tafiya kasashen waje ko asibitoci masu zaman kansu da su yi amfani da wannan dama don zuwa asibitin Jami’ar Ahmadu Bello wajen gudanar masu da wannan sabuwar fasaha.