✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Riƙaƙƙun ’yan daba da dilolin ƙwaya 31 sun shiga hannu a Kano

Kwamitin ya ce zai ci gaba da yaƙi da irin waɗannan ɓata-gari don ganin jihar ta zauna lafiya.

Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano kan Tsaro da Gyaran Matasa, ya kama ’yan daba 31 a wani samame da ya gudana a unguwanni bakwai a jihar.

An kai samamen ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Mayu, 2025 ƙarƙashin jagorancin Dokta Yusuf Ibrahim Kofar Mata.

Unguwannin da aka kai samamen sun haɗa da Ɗorayi, Ja’in, Sharada, Unguwar Dabai, Dukawa, Kabuga, Kofar Mata da sauransu, wuraren da suka yi ƙaurin suna wajen aikata laifuka.

Daga cikin waɗanda aka kama, mutum 25 ana zargin ’yan daba ne, yayin da shida ake zarginsu dallacin miyagun ƙwayoyi.

A cikin kayan da jami’an suka ƙwato akwai bindigogi na gargajiya guda huɗu, wuƙaƙe da adduna tara, sanduna uku, tabar wiwi da kuma ƙwayoyi irin su Exol guda 173 da wasu miyagun ƙwayoyi daban-daban.

Haka kuma, jami’an sun kama wasu riƙaƙƙun ’yan daba da suka daɗe suna addabar al’ummar Dorayi, ciki har da Dan Abba, Bola, Baka Kashi, Ramos, Abba Maciji da Abdul Baki.

“Dukkanin ’yan daban 25 da muka kama an gurfanar da su a gaban Kotun Majistare mai lamba 16 da ke kan titin Zungeru, kuma an tasa ƙeyarsu zuwa gidan gyaran hali.

“Sauran masu sayar da ƙwayoyi guda shida, ciki har da Rabi’u Hamza, an miƙa su ga hukumar NDLEA don ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a kotu,” in ji Dokta Kofar Mata.

Ya bayyana wannan samame a matsayin babban ci gaba wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Ya ce unguwanni kamar Dorayi sun sha fama da rikice-rikicen faɗan daba sama da shekaru 20.

Kama waɗannan ɓata-gari zai iya kawo ƙarshen wannan matsala.

Ya ƙara da cewa kwamitin ya ƙunshi jami’an tsaro da jami’an gwamnati domin haɗa kai wajen tsaftace birnin Kano da kuma taimaka wa matasan da suka ɓace su koma turbar gaskiya.

“Kwamitin Haɗin Gwiwa zai ci gaba da jajircewa domin ganin an samar da ingantaccen tsaro da kuma zaman lafiya ba tare da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ba a Kano,” in ji kwamitin.

Ga hotunan wasu daga cikin kayan da kwamitin ya ƙwato: