Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta ceto wata tsohuwa mai shekaru 80 da aka sace a Jihar Kano, bayan wani samame da suka kai Ƙaramar Hukumar Garki.
A yayin samamen, sun kashe mutane biyar da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sannan sun kama wasu biyar.
- Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa
- Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso
Rahoton ya ce samamen ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar 16 ga watan Mayu, 2025 bayan samun sahihan bayanan sirri.
Waɗanda suka sace tsohuwar, Hajiya Hajara daga Ƙaramar Hukumar Minjibir, a Jihar Kano, su 12 ne ɗauke da bindigogi, kuma sun zo ne a kan babura.
Rundunar ta haɗa kai da jami’an ’yan sanda daga Gagarawa, Gumel, Garki, da Sule-Tankarkar tare da ‘yan banga da mafarauta, ƙarƙashin jagorancin ACP Bala Umar, kwamandan ’yan sandan yankin Gumel.
Sun kai farmaki maɓoyar ’yan ta’addan da ke Wadi Fulani, GGW Tagwayen Fage, Wusada Fulani da Katoro Fulani duka a Garki.
A nan ne suka kashe mutum biyar da ake zargi, sannan suka kama wasu biyar ciki har da sarkin Fulanin Katoro mai suna Yahaya mai shekara 35.
Sun ceto Hajiya Hajara cikin ƙoshin lafiya, sannan sun ƙwato bindigogi guda uku (AK-47 biyu da LAR daya), harsashi 14, babura biyu da wayoyin hannu biyu.
Gawarwakin waɗanda aka kashe an kai su asibitin Gumel don gudanar da bincike, kuma babu jami’in tsaron da ya rasa ransa.
Majiyoyi sun ce ba a biya kuɗin fansa ba kafin ceto tsohuwar.