Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta dakatar da haska shirin Labarina, Dadin Kowa da wasu ƙarin fina-finan Hausa guda 20 a kafafen Internet ko gidajen talabijin.
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne a ƙoƙarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara dora masana’antar Kannywood a kan saiti.
A cewar wata sanarwar da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar da daren Lahadi, fina-finan da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Labarina, Dadin Kowa, Manyan Mata, Garwashi, Jamilun Jidda da kuma Gidan Sarauta.
Sanarwar ta ce umarnin ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, bayan wani zamanta da kuma tattaunawar da ta gudanar.
- An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja
- Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa
Jerin fina-finan da aka dakatar
Sanarwar ta bayyana jerin fina-finan da dakatarwar kamar haka:
- Ɗakin Amarya
- Mashahuri
- Wasiyya
- Tawakkaltu
- Mijina
- Wani Zamani
- Mallaka
- Kuɗin Ruwa
- Boka Ko Malam
- Wa Ya San Gobe
- Rana Dubu
- Manyan Mata
- Fatake
- Gwarwashi
- Jamilun Jiddan
- Shahadar Nabila
- Daɗin Kowa
- Tabarma
- Kishiyata da kuma
- Rigar Aro.
Hukumar ta ce ta ɗauki gagarumin matakin ne domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ƙa’idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne fim gabanta a tantance shi kafin a sake shi.
Sanarwar ta kuma ce doka ce ta ba Hukumar damar tace duk wani fim tare da lura da ayyukan ’yan masana’antar Kannywood matukar suna da rajista da hukumar a ko ina suke.
“A saboda haka, ana shawartar masu ɗaukar nauyin waɗannan fina-finai da su tabbatar da sun bi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka wannan fina-finai a gidajen talabijin ko kafar internet.
“Haka kuma ana sanar da su cewa su miko fina-finansu ga hukumar domin tantance su tare da ba su shaidar inganci ta tacewa nan da sati ɗaya mai zuwa wato daga Litinin, 19 ga watan Mayu, 2025 zuwa 25 ga Mayu, 2025 domin gujewa fushin doka,” in ji sanarwar.
Tun bayan canjin da kasuwar fina-finai dai ta samu da ya sa kuɗaɗen da ake samu a sayar da fina-finai suka yi ƙasa sosai, galibin ’yan masana’antar Kannywood suka koma shirya fina-finai masu dogon zango domin a ci gaba da damawa da su.
Akan ɗora fina-finan ne a dandalin YouTube da wasu gidajen talabijin a mako-mako.