✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa zare tsakanin ‘yan Kannywood da Alhikima

Tauraron Kannywood kuma mai sayar da maganin gargajiya, Abdullahi Alhikima ya magantu bayan da wasu ‘yan Kannywood suka caccake shi kan kalaman da ya yi…

Tauraron Kannywood kuma mai sayar da maganin gargajiya, Abdullahi Alhikima ya magantu bayan da wasu ‘yan Kannywood suka caccake shi kan kalaman da ya yi a kansu.

Aminiya ta rawaito cewa hatsaniyar ta samo asali ne bayan fitattun ‘yan Kannywood da suka hada da Abdul M Sharif, Nura M Inuwa, Abubakar Bashir Maishadda, Sadik Sani Sadik, da sauransu suka kai wa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar ziyarar goyon baya.

Wannan ya tunzura Alhikma kasancewar wasu daga cikin wadanda suka je mubayi’ar ‘ya’yan kungiyar YBN ne a baya, da kuma 13/13 ta ubangidansa, mawaki Rarara.

A cikin wadanda Alhikima ya caccaka har da Shugaban Hukumar Fina-finai ta Ƙasa, Ali Nuhu.

Sai dai a kan hakan ne kuma wasu ke hasashen lallai ta tabbata alaƙa ta yi tsami tsakanin Alin da Rarara, wadanda a da suke abokai.

To sai dai Alhikman ya yi mi’ara koma baya, inda a ranar Laraba ya fito yana bayar da haƙuri, a cikin wani bidiyo da ya karade soshiyal midiya.

“Ina amfani da wannan dama domin janye kalamaina, na kuma bayar da hakuri ga ‘yan masana’antar Kannywood. Na yi wasu maganganu kuma zan janye bisa dalilai guda uku.

“Na farko maganar da na yi wasu na ganin ciyaman Alhaji Dauda Kahutu Rarara shi ne ya saka ni na yi wannan maganar. Ina ba da hakuri domin barranta shi da ita, domin ni na yi ta. Domin ya kira ni ya kuma nuna min kuskuren da ke cikin maganganuna. Kuma dama cikar dan adam shi ne idan shugabanka ya ce ka yi daidai ka karbi daidai ne. Idan shugabanka ya ce kayi kuskure ka karba.

“Haka kuma akwai abokiyar aikina Aishatul Humaira ta zaunar da ni ta gwada min kurakuran da ke cikin maganar da na yi, musamman a kan mai girma MD, Ali Nuhu. Wanda uba ne a wurinta a masana’antar. Hallau a cikin masana’antar tana da aminai maza da mata wanda suke da alaka ta mutunci da mutunta juna.”

Sai dai Alhikma ya yi togaciya a ban hakurin nasa, in da ya ce iya ‘yan Kannywood zai bai wa hakuri ban da wadanda ya kira da ‘yan shisshigi’.

Ita ma dai Aishatul Humairan ta bai wa ‘yan Kannywood din hakuri duk da ba da yawunta Alhikima ya tayar da hazon ba,  musamman Ali Nuhu, wanda ta ce uba ne a gare ta.