Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta sanar da dakatar da duk wani nau’in tallan magungunan gargajiya a cikin fina-finai, a kan titi ko amfani da lasifika.
Wannan na cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, wadda Jami’in Yaɗa Labaran Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya raba wa manema labarai.
- ’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano
- Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja
Shugaban hukumar ya ce wannan matakin na da nufin kare martabar masana’antar fina-finai da kuma tabbatar da cewa duk wani bayani da ke zuwa ga jama’a ya bi ƙa’idoji da doka.
“Yawancin tallace-tallacen maganin gargajiya da ake yi a tituna ko kuma a cikin fina-finai suna karya dokokin da hukumarmu ta gindaya.
“Wannan dalili ne ya sa muka ɗauki matakin dakatar da duk wata hanya da ake amfani da ita wajen wannan talla, har sai mun tantance su tare da bayar da sahalewa,” in ji El-Mustapha.
Hukumar ta bayyana cewa daga ranar Laraba, 21 ga watan Mayu, 2025, duk masu ruwa da tsaki a harkar maganin gargajiya dole ne su miƙa tsarin tallace-tallacensu domin tantancewa cikin mako guda, ko kuma su fuskanci hukuncin hukumar.
“Mun bai wa kowa kwana bakwai ya gabatar da tsarin tallarsa domin mu duba.
“Wannan ya shafi masu fina-finai da kuma waɗanda ke yawo da lasifika a titi. Doka za ta ɗauki mataki a kan duk wanda ya saɓa,” cewar El-Mustapha.
A cikin wannan sanarwar, shugaban hukumar ya kuma buƙaci haɗin gwiwar tashoshin talabijin da Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC), domin ganin an daƙile abin da ka iya shafar tarbiyya da lafiyar al’umma.
“Muna kira ga tashoshin talabijin da hukumar NBC su mara mana baya wajen tabbatar da bin doka da oda a fannin yaɗa bayanai, musamman masu nasaba da magunguna da lafiya. Wannan zai taimaka wajen kare martabar fina-finai da kuma lafiyar al’umma,” in ji shi.