An gudanar da jana’izar Malam Maikudi Umar (Cashman) Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a garin Zariya, Jihar Kaduna.
Marigayi Maikudi Umar (Cashman) dan shekaru 62, jarumi ne, mai shirya finafinai kuma ma darakta da ke gudanar da harkokinsa a a masana’antar Kannywood da Nollywood.
Har ila yau malami ne a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya.
Dan uwan mamacin, Abdul Azeez Muazu, Talban Tudun Jukun ya ce Umar ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a Asibitin Koyarwa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya.
- An kama matashi da ya yi shigar mata a Adamawa
- Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum
Aminiya ta ruwaito cewa Cashman ya rasu ne a daren ranar Laraba, amma aka gudanar jana’izarsa a ranar Alhamis a Zariya.
Ya rasu ya bar yan uwanshi da dama