Sanatan Kaduna ta Kudu, Sunday Marshall Katung, ya ce zai yi aiki tare da sauran ’yan majalisar tarayya daga jihar domin tabbatar da cewa wadanda harin bam da sojoji suka kai a yankin Tudun Biri da ke jihar adalci.
Rundunar sojin Najeriya a ranar Litinin ta dauki alhakin kai hari da jirgi mara matuki, a lokacin da dakarunta ke fatattakar ’‘yan ta’adda a gundumar Afaka a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
- Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3, sun kama 6 a Kaduna
- Ba za mu yafe jinin masu Mauludi da sojoji suka kashe ba —Sheikh Jingir
Rundunar sojin ta ce lamarin ya faru ne bisa kuskure a maimakon jefa bam ga ’yan ta’adda sai aka jefa kan masu taron Mauludi.
A sanarwar jajensa ga al’ummar Jihar Kaduna, Sanata Katung ya ce za su tabbatar da kula da lafiyar wadanda suka jikkata.
“Wannan lamarin abun takaici ne da kuma koma baya ga yankin, Jihar Kaduna da ma kasa baki daya,” in ji shi.
Haka kuma, Sanata Babangida Hussaini daga Jigawa ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.
A cikin wasikar ta’aziyya ga Sanata Lawal Adamu Usman (Kaduna ta Tsakiya) da al’ummar mazabarsa, Hussaini ya ce cikin kaduwa, ya bayyana takaicinsa kan faruwar lamarin.