✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu yafe jinin masu Mauludi da sojoji suka kashe ba —Sheikh Jingir

Sheikh Jingir ya ce kada Gwamnati ta ce a bar wa Allah, domin Allah Ya yi umarnin a hukumta duk wanda ya aikata irin wannan…

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce kada Gwamnati ta kawo maganar neman a bar wa Allah kisan da sojoji suka yi wa  Musulunci a taron Mauludi a Jihar Kaduna, domin Allah ne Ya yi umarnin a hukumta duk wanda ya aikata irin haka.

Sheikh Jingir ya bukaci Rundunar Sojin Najeriya da Gwamnatin Tarayya su yi kwakkwaran bincike kan sojojin da suke da hannu a kai hari ga al’ummar Musulmi a kauyen Tudun biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Jagoran kungiyar Izalan ya ce wannan kisan gilla da aka yi wa wadannan bayin Allah, abu ne wanda ba za a taba amince da shi ba, don haka bai kamata a bar shi ya tafi a banza ba, ba tare da an hukumta wadanda suka aikata wannan aika-aika ba.

“A hukumta duk wanda aka samu da hanu a wannan al’amari. Kada Gwamnati ta ce a bar wa Allah, domin Allah Ya yi umarnin a hukumta duk wanda ya aikata irin wannan al’amari,” in ji shi.

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana wannan bukata ce a wajen wani taron ’yan jarida da ya kira a gidansa da ke garin Jos.

Sheikh Jingir ya ce aikin kowane irin shugaba ne ya kare rayukan al’ummar da ya ke yiwa Shugabanci.

Don haka, hukumta wadanda suka kashe bayin Allah wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, shi ne kyakkyawan shugabanci.

Ya ce Allah Ya haramta kisan bayin Allah, ko Musulmi ne ko Kirista ne ko wanda ba shi da addini ne, domin yana da daraja da ’yancin rayuwa, a wajen Allah.

Ya kara da cewa, “Tun da rundunar Sojan Najeriya sun amince cewa su ne suka kawo wannan hari, hakan ba zai sanya mu ce da niyya aka kawo wannan hari ba?

“A duk lokacin da rundunar sojan Najeriya da hukumar tsaron farin kaya ta SSS da rundunar ’yan sandan da Jami’an Hukumar hana fasa kauri da jmi’an sige da fice za su gudanar da ayyukansu, wajibi ne su tsara yadda za su gudanar da ayyukansu, domin gudun kada bata-garin cikinsu, su bata masu ayyukan nasu.

“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kafa kwakkwaran Kwamitin bincike, wanda zai binciko ainihin abin da ya faru kan wannan hari da aka kawo.

“A hukumta duk wanda aka samu da hanu a wannan al’amari. Kada Gwamnati ta ce a bar wa Allah, domin Allah Ya yi umarnin a hukumta duk wanda ya aikata irin wannan al’amari.”

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana wannan bukata ce a wajen wani taron ’yan jarida da ya kira a gidansa da ke garin Jos.

Daga nan ya misa sakon ta’aziyarsa, ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar da Mai Martaba Sarkin Zazzau da Gwamnan Jihar Kaduna da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan hari.