✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dahiru Bauchi ya nemi Tinubu ya biya jinin Musulmin da jirgin soji ya kashe a Kaduna

Sheikh Dahiru Bauchi ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi bincike, da kuma biyan hakki da diyyar Musulumin da jirgin soya ya kashe a Kaduna

Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya roki Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da an gudanar da cikakken bincike tare da biyan diyya ga iyalan al’ummar Musulmin da sojojin Najeriya suka kashe a harin bom da aka kai a yankin Tundun Biri da ke jihar Kaduna a ranar Lahadi a yayin bikin maulidi na murnan haihuwar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama.

Dahiru Bauchi ya yi wannan kiran ne a yau Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi.

Shehin malamin ya ce, “Muna so Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ta jajirce wajen tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa da aka kashe a wajen bikin Mauludi, tare da hukunta jami’an da suka aikata wannan ta’asa.

“Ya kamata gwamnati ta yi aiki tukuru don hana abubuwan da ke faruwa a nan gaba, da kuma kiyaye rayukan yan Nijeriya da yake salwanta?

“A kare musu mutuncinsu, kare hakkinsu na rayuwa a matsayinsu na ’yan Adam, a kare musu ’yancinsu na yin addininsu ba tare da tsangwama ba da kuma kiyaye hakkin ɗan adam da dokokin ɗan adam na duniya.”

Ya miqa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da daukacin al’ummar Musulmin duniya da ma na Afirka, ya kuma yi addu’ar Allah Ya jiKan su Ya gafarta musu, ya kuma ba mu haKurIn jure rashinsu.

Malamin ya ce, “Muna cikin bakin ciki, yadda mutanen da ke sama suke jefa bam ga wadanda ba su ji ba ba su gani ba, laifin wane ne? Laifin gwamnati ne ko laifin wane ne?

“Bai kamata a rika yin wasa da rayukan jama’a ba, mun bukaci a gudanar da cikakken bincike a kan wannan bala’in da ya kashe mutane da dama da ba su ji ba ba su gani ba.”

Ya ce, “Mun fara tattaunawa da gwamnatin tarayya ta hannun Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, ya kuma yi alkawarin cewa za su tabbatar sun yi bincike tare da yin adalci ga wadanda abin ya shafa idan shugaban ya dawo daga tafiyarsa.

Dahiru Bauchi ya ce, gudanar da cikakken bincike kan tashin bam din da aka ce ba gangan ba ne yana da matukar muhimmanci wajen dakile yawan faruwar wadannan hadurra a nan gaba ta hanyar nazarin yanayin da ya haifar da wannan musiba, “domin a baya an kashe wasu Musulmin da ba su ji ba ba su gani ba a lokacin da suke kan hanyar komawa gida an kai musu hari aka kashe su a Jos da kuma hari na baya-bayan nan da suka jefa da bam din da ya kashe su ba za mu amince da hakan ba”.