A yau Talata Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya domin zuwa kasar Netherlands ziyarar aiki.
Kakakin shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya sanar cewa Tinubu ya amsa gayyatar da firaministan kasar Netherlands, Mark Rutte ya yi masa ne.
Ya ce daga Netherlands, Tinubu je taro na musamman kan Tattalin Arzikin Duniya (WEF) da aka shirya gudanarwa a ranakun 28 da 29 ga watan nan na Afrilu a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
Ngelale ya ce, yayin ziyarar a Netherlands, shugaba Tinubu zai tattauna da firaminista Mark Rutte, da kuma Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima.
- Majalisa ta gayyaci minista da NERC kan karin kudin lantarki
- NAJERIYA A YAU: Matakan Kauce Wa Yaɗuwar Cutuka A Makarantu Saboda Tsananin Zafi
Sarauniyar ita ce mai ba da shawara ta musamman ga Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin Kudi da cigabansu (UNSGSA).
- NAJERIYA A YAU: Matakan Kauce Wa a Yaɗuwar Cutuka A Makarantu Saboda Tsananin Zafi
- Majalisa ta gayyaci minista da NERC kan karin kudin lantarki
“Yayin ziyarar a kasar Netherlands, shugaban kasa zai halarci taron kasuwanci da zuba jari na kasashen biyu inda za su lalubo bangarorin hadin gwiwa da karfafa juna, musamman a fannin noma da kula da dabarun kula da ruwa.
“Taron Kwamitin Tattalin Arzikin na Duniya zai mayar da hankali kan Haɗin gwiwa da hanyoyin kawo cigaban makamashi, inda Tinubu da mukarrabansa za su tattauna da mahalarta daga sauran ƙasashe a kan harkokin kasuwanci.
“Shugaban zai samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami’an gwamnatinsa,” inji Ajuri Ngelale