Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewar har yanzu Gwamnatin Tarayya na biyan kuɗin tallafin man fetur.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, inda ya ce Gwamnatin Tarayya na kashe maƙudan kuɗi fiye da wanda ta yi a baya a matsayin tallafin man fetur.
- Yadda aka yi jana’izar ’ya’ya 6 na mutum 1 a Gombe
- Masu iƙirarin dakatar da Ganduje ba ’yan Jam’iyya ba ne —APC
Idan ba a manta ba, Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana cire tallafin man fetur a jawabinsa na farko, bayan karɓar mulki a watan Mayun 2023.
Sai dai El-Rufai, ya ce yana goyon bayan cire tallafin mane fetur ɗin, inda ya bayyana cewa tsarin biyan tallafin na baya na buƙatar sauye-sauye.
A cewarsa gwamnatin ta yi abin da ya dace game da cire tallafin man fetur ɗin.
“Tallafin man fetur wata doka ce da shugaban ƙasa ke aiwatarwa, kuma yana d kyau da aka cire tallafin man fetur.
“Sai dai a yanzu gwamnati na biyan tallafin man fetur fiye da yadda ta ke biya a baya.
“Idan mutane suna so su gane yadda ake biyan tallafin man fetur ɗin, sai su kwatanta yadda farashin man fetur da na dizal yake, wanda a ƙa’ida ya kamata a ce farashin fetur ya haura Naira 1000 kan kowace lita,” in ji shi.
El-Rufai ya bayyana cewa mutane da yawa ba su san gwamnati na ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.
Ya ce idan mutane suna so buƙatar sanin ko ana biyan tallafin, kamata ya yi su kwatanta farashin man fetur da na dizal.
A cewarsa farashin fetur ya kamata ya fi na dizal tsada wanda a yanzu ya haura Naira 1000 kan kowace lita, amma sai gashi ana sayar da fetur kan Naira 600 a kowace lita.
El-Rufai, ya gabatar da wata takarda a taron ƙara wa juna sani kan makamar aiki da aka shirya wa manyan jami’an gwamnatin Jihar Borno.