✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar ’ya’ya 6 na mutum 1 a Gombe

Mutum shida ’ya’yan mutum daya sun rasu a hatsarin mota a Jihar Gombe

Wasu mutum shida ’ya’yan mutum daya sun rasu a sakamakon hatsarin mota a Jihar Gombe.

Mahaifinsu mamatan shi ne Mai Dalan Gombe, kuma sun gamu da ajalinsu a hatsarin da ya rutsa da su a kan hanyar Azare zuwa Gombe a ranar Lahadi.

Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa Fadar Sarkin Gombe, Alhaji Dokta Abubakar Shehu Abubakar III inda suka halarci sallar jana’izar.

Sakon ta’aziyyarsa mai dauke da sanya hannun babban baraktan yada labarai na fadar gwamantin jihar, Isma’ila Uba Misilli, ta nuna kaduwar gwamnan bisa wannan rashi a sanadiyar hatsarin mota.

“Rasa ’ya’ya shida a lokaci daya ba karamin tashin hankali ba ne inda ya hori mahaifin mamatan da ya yi tawakkali sannan ya yi musu addu’ar Allah Ya sa Aljanna ce makoma a gare su.”