Ana zargin wani direban tirela ya gudu da buhunan masara 463 da aka aike shi da su, bayan da ya bai wa ɗan rakiyarsa guba a cikin shayi a yankin Maraban Jos da ke Jihar Kaduna.
Wani ɗan kasuwa da ke safarar hatsi daga Jihar Kano zuwa kamfanoni a sassa daban-daban na Nijeriya, Injiniya Jamilu Haruna, ya shaida wa Aminiya cewa direban da ya ɗora wa masara buhu 463 domin kaiwa kamfanin Olam da ke Ilorin a Jihar Kwara, ya gudu da kayan.
“Kuɗin kayan sun kama Naira miliyan miliyan ashirin da ɗaya da dubu ɗari shida da tamanin da shida da ɗari huɗu.
“Wallahi jarin nawa ke nan ɗungurungum na dora a motar,” in ji ɗan kasuwar, wanda ya bayyana cewa direban ya ɗauko masa masarar ce a cikin tirela ƙirar Hoho mai taya 18 daga yankin Doguwa a Jihar Kano.
Ya ƙara da cewa direban ya sami nasarar guduwa da kayan ne bayan da ya ba wa mutumin da aka haɗa shi da shi a matsayin ɗan rakiya guba a shayi, sannan ya jefar da shi ya gudu da motar maƙare da kayan.
- Yadda aka kama ɗan bindiga ɗauke da N13m a hanyar Jos
- Ɗalibi ya ƙone budurwarsa mai tsohon ciki har lahira
“Dukkanin buhunan 463 na masara da wobil ɗin kayan ya kwashe da su ya tsere. Wasu jami’an ’yan kamasho da suka saba sama mana motocin haya sun shiga cikin binciken. Haka nan ’yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike don gano inda direban yake,” in ji ɗan kasuwar.
A zantawarsa da Aminiya, Injiniya Jamilu, ya ce tun bayan faruwar lamarin har yanzu ba a sami gano direban ba balantana kayan, lamarin da ya ce ya yi sanadiyyar raba shi da duk jarin da yake juyawa.
Yadda abin ya faru — Mai kaya
Ya ce, “Mukan yi safarar masara mu kai wa kamfanoni a Kano da ma maƙwabtan jihohi, wacce muke siye a kasuwannin yankin Doguwa da Tudun Wada a Kano da kuma Saminaka a Jihar Kaduna.
“A wasu lokutan idan kayan suka yi yawa a wasu sassan na Arewacin Nijeriya, mukan kai kaya har irin su jihohin Kwara da Oyo da ma Legas.
“Wannan karon na haɗa kaya buhu 463, sai na sa ’yan kamasho a Unguwar Bawa su kawo min mota. To su akwai hanyar da suke bi su tantance sahihancin direba kafin su haɗa mu da shi, don mu ba huruminmu ba ne.
“To a haka ne ’yan kamasho suka samo mana direba, muka yi cinikin kuɗin mota Naira miliyan ɗaya da dubu hamsin. Aka kawo min mota muka loda kaya a kan za a kai su Ilorin. Kuɗin kayan kuma sun kama Naira miliyan 21,640. Wallahi jarin nawa ke nan ɗungurungum na dora a motar,” in ji shi.
Ya ce sukan haɗa direban da aka ba su da amintaccen ɗan rakiya daga wajensu, “saboda gudun halin wasu direbobin na yi wa kayan da aka ɗora musu ɗauki ɗai-ɗai idan babu idon mai kaya ko wakilinsa.”
Injiniya Jamilu ya ce, “Direban da ɗan rakiyar sun tashi da kayan daga Doguwa suka kwana a Unguwar Bawa saboda dare ya yi, gari na wayewa suka shiga Marabar Jos a Kaduna, sai direban ya ce su tsaya su yi gyaran ƙafar motar saboda sun ɗan shiga ramuka.
“A nan ne ma direban ya kira ni ya ce akwai ragowar cikon kuɗinsa Naira 350,000, na tura masa N100,000 zai yi gyara, na tura masa kuma muka yi waya da ɗan rakiyata ya ce lafiya kalau,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “To tun wannan ranar ta 25 ga watan Yunin 2025 ban sake jin ɗuriyarsu ba. Na yi ta kiran yaron nawa da shi direban amma ba na samun su. Har gari ya waye ina kira ban samu ba, sai na ɗauka ko sun shiga wuraren da hanya babu kyau ne ko kuma babu sabis.
“Kawai sai ga ɗan sanda ƙashegari ya zo gidana ya ce akwai wani yarona da aka tsinta
a sume, ‘an tsince shi ya biyo kaya za su Ilorin, sai direba ya ba shi shayi, tun da ya sha kuma a nan ya faɗi ya sume, mu kuma washegari muka zo muka gan shi, shi ne muka ɗauke shi muka kai asibiti, inda bayan ya farfaɗo ya ce mana daga Doguwa yake, ya biyo kayanka ne’.
“Da suka yi wannan bayanin ne na tabbatar musu da cewa kayana ne. Shi ɗan sandan da ya kawo mana wannan mutumin ma shi ne ya je ya kamo mana wannan ɗan kamashon da tun
Direban ya yi layar zana
ɗan kasuwar ya ƙara da cewa tun daga nan ne ma suka gano duk lambobin direban ma tuni ya watsar da su ya canza wasu, kuma har yanzu duk hanyoyin da suka bi “mun kasa gano ainihin lambar wayarsa, ko kuma motar.”
Sai dai ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ɗan kamashon yake samo masa motar ɗaukar kayan ba, domin a iya bana ya ba shi mota sama da guda 11.
Amma ya ce, “Shi ma ɗan kamashon wani ya hada shi da direban, kuma wanda ya haɗa sun ma shi ma bai san ainihin adireshin direban ba.” Sai dai ya ce yanzu haka ɗan kamashon da kuma wanda ya haɗa shi da direban suna tsare a hannun ’yan sanda yayin da ake ci gaba da faɗaɗa bincike.
Injiniya Jamilu ya ce, “Shi kansa yaron motar da aka ba gubar sannan aka jefar da shi ya sha bin kayan a baya kuma an kai su lafiya, wannan ne karo na farko da aka sami matsala.
‘Na rungumi ƙaddara’
“Na ɗauki wannan a matsayin jarrabawa, amma ina ci gaba da addu’ar idan da rabo Allah Ya bayyana kayan, idan kuma babu, Allah Ya mayar min da mafi alheri,” in ji ɗan kasuwar.
Ya ce yanzu haka ’yan sanda na ci gaba da bincike a ƙarƙashin ofishin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda na Shiyyar Tudun Wada da ke Jihar Kano.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba shi da masaniya a kan lamarin, amma ya ba shi lokaci zai bincika.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ya ce yana kan binciken bai kai ga samun cikakken bayani a kan lamarin ba.