Wasu kananan yara biyar sun mutu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a harabar wani gida a yankin Agyaragu da ke Karamar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa.
Yaran sun rasu ne a sakamakon daukewar nunfashinsu a cikin motar, lamarin da ya jefa mazauna yakin yankin, wadanda yawancinsu manoman ne, daga kabilu daban-daban, cikin alhini.
An gano gawarwakinsu ne da misalin karfe 1 na rana a cikin motar bayan mutanen yankin sun shafe tsawon lokaci ana neman su.
Misis Ifeoma Nnaji, wacce ta rasa ’ya’yanta biyu, Nmesoma da Chidima, ta bayyana yadda aka gano gawarwakin ta ce, “Mun duba ko’ina… Daga karshe, wani ya ba da shawarar mu duba motar da aka yi watsi da ita, kuma a can muka same su, babu rai,” in ji ta cikin kuka.
- Yadda rashin wutar lantarki ke ajalin rayuka a manyan asibitoci
- Masana sun ƙalubalanci sojoji kan maharan ƙasashen waje
- NAJERIYA A YAU: Abin ya sa aka kasa kawo ƙarshen Tamowa a Arewa Maso Gabas
Ta bayyana cewa motar ta dade da ajiye a gidansu kuma a kullum a kulle take.
Misis Bridget Iormagh, kakar Eunice Shapera mai shekaru biyar, ta bayyana bakin cikinta, ta ce, “A kullum tana kusa da kofar gidana… Amma a wannan ranar, Eunice ta bi sauran yaran suka tafi wasa.” Wani makwabci ne ya gano yaran a cikin motar da aka yi watsi da ita.
Wannan mummunan lamari shi ne irinsa na uku da ya faru a Jihar Nasarawa a ’yan shekarun nan, inad a watan Agustan shekarar 2013, wasu biyu sun mutu a watan Agustan 2019 a Keffi.
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasa ’ya’yansu. Mataimakin Gwamna Dakta Emmanuel Akabe ya jagoranci tawagar da ta kai ziyarar ta’aziyya ga yankin, inda ya bayyana lamarin a matsayin “mai karya zuciya da kuma bakin ciki.”
Ya kuma yi kira ga iyalan da su dauki wannan babban rashin a matsayin kaddara daga Allah.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun samu rahoton ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi.
Ya kara da cewa an tabbatar da mutuwar yaran a Asibitin Aro sakamakon shakewar numfashi, kuma an fara cikakken bincike don gano yadda yaran suka samu shiga motar.
Hukumomi na kira ga iyaye da masu ababen hawa da su kara kula da ’ya’yansu da kuma tabbatar da cewa yara ba za su iya shiga motocin da aka ajiye ko kuma aka yi watsi da su ba, domin kauce wa irin wannan bala’i a nan gaba.