Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun yi barazanar shiga yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja, Kogi, Nasarawa da Jihar Neja cikin duhu.
Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024.
- A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates
- Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu
Ƙorafe-ƙorafen nasu sun haɗa da rashin biyan kuɗin fansho na tsawon watanni 16, rashin ƙarin girma, rashin kula da lafiyar ma’aikata.
Sun kuma ce an ƙi biyansu ladan aiki na shekarar 2024 duk da cewa sun taimaka wajen samar da kuɗin shiga har Naira biliyan 94 cikin watanni uku.
“Mun yarda mun dakatar da yajin aiki a watan Nuwamban 2024 saboda alƙawuran da kamfanin ya ɗauka, amma har yanzu ba a aiwatar da su ba,” in ji jagoran ƙungiyar, Opaluwa Eleojo Simeon.
“Ma’aikata suna fama da matsin lamba da rashin kulawa, har wasu na mutuwa saboda halin da suke ciki.”
Rosemary Odeh, wata shugabar ƙungiyar, ta ƙara da cewa: “Mun shirya komawa yajin aiki a kowane lokaci. Ba za mu ja da baya ba har sai mun samu adalci. Wannan gwagwarmaya ba za ta tsaya ba.”
Ƙungiyoyin sun umarci mambobinsu da su fara shiri a dukkanin yankunan AEDC.
Idan aka fara yajin aikin, al’umma a yankunan da abin ya shafa na iya fuskantar rashin wutar lantarki na tsawon lokacin yajin aikin zai shafe.