Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri.
Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
- Ganduje ya halarci Majalisar Wakilai don sheda ’Yan Majalisa 2 zuwa APC
- Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato
Kakakin ya ce an kama Fatima ne da laifin safarar alburusai ta yankin Keana da Doma a cikin Jihar Nasarawa don taimakon masu aikata laifuka a Katsina, inda take zaune.
“Cikin gaggawa kan bayanan sirri da aka samu, Kwamishinan ’yan sanda CP Shetima J. Mohammed, ya ba da umarnin tura sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane na rundunar cikin gaggawa.
“Tawagar ta yi aiki tuƙuru, wanda ya kai ga kama wanda ake zargin tare da ƙwato alburusai 400 ƙirar 7.62ɗ39mm da harsashi 81 na 7.62mm na NATO.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A yanzu haka ana tsare da wanda ake zargin kuma ana yi mata tambayoyi mai tsanani yayin da masu bincike ke ƙoƙarin tarwatsa cibiyar safarar makamai da kuma gano alaƙarta da ’yan fashi da makami da ta’addanci.”
Nansel ya bayyana cewa, kama matar yana wakiltar wani babban ci gaba a yaƙi da safarar makamai da aikata laifuka a yankin.