A bidiyon da wani mai suna Nawab Sheikh ya fitar na nuna yadda ya hau motarsa, wacce yake tuka ta a kan titunan birnin Murshidabad a cikin ƙasar Indiya, don nishaɗantar da mahaya babur, wanda ya sa bidiyon yake ta yaɗuwa a shafin sada zumunta na Instagram.
Babu wani wuri mafi kyawun nuna bajintar kirkira don jan hankalin ɗan Adam kamar intanet.
Haka kuma idan aka zo fannin ƙirƙirar sabuwar fasaha, ba da yawa ba ne ke irin wannan a cikin Indiyawa.
Na baya-bayan nan shi ne ƙirƙirar da wani mutumin West Bengal – “motar gado” inda ya mai da gadonsa ya koma mota kuma yake tuka ta.
Bidiyon Nawab Sheikh a motar da yake yawo a kan titunan Murshidabad don nishaɗantar da mahaya babur yana yaɗuwa a shafukan Instagram.
Bidiyon ya nuna wani gado da aka mayar zuwa motar tafi da gidanka, mai taya hudu da birki.
Direban motar ne ke sarrafa ta kuma ana sarrafa ta, ta tsarin tuki da sitiyari.
Bayan saka katifa da zanin gado da matashin kai, gadon yana da ƙarin ƙirƙira ta musamman: wanda akwai madubin gefe da ke manne da kowane gefe don taimakon direban kallon bayansa.
Masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani sun yi ta tururuwa wajen yin sharhi, inda suka tofa albarkacin bakinsu a kan wannan kirkira ta musamman.
Wani mai amfani da shafukan ya rubuta, “Indiya ba ta ’yan koyo ba ce.”
Wani mai amfani da shafukan na biyu ya yi dariya, sannan kuma ya aika da alamar dariya.
“Ana iya ganin irin wannan ne a Indiya kawai,” in ji na uku.
Wani mai amfani da manhajar sada zumunta ta X, kodayake ya yi suka kuma ya rubuta, “Shin yana da takardun da ake bukata da amincewa daga sashen hukuma don tuka irin wannan abin hawa a kan hanya?
“Mutane sukan yi watsi da ka’idojin tuki, kawai don son rai.”
“Idan wannan motar ta Nawab ta haifar da wasu hadura fa? Dokokin zirgazirga sun yarda da haka? Ko kuma irin wannan motar ce ake yin gwaji?” wani ya tambaya.
A cewar jaridar Times of India, Mista Sheikh ya kwashe sama da shekara guda yana zuba jarin Naira miliyan 3 don ƙirƙirar wannan motar sannan ya wallafa a dandalin sada zumunta.
Duk da samun karɓuwa da yawa na tukin motar gado a kan tituna, ’yan sanda sun ja motar da ke kan gadon, har ma suka tarwatsa ta saboda matsalar cunkoson ababen hawa a hanyar Jihar Raninagar Domkal.
Sai dai a baya can, akwai wani mutumin Delhi da ya taba canza mota ƙirar Maruti Suzuki Jimny zuwa gado.