✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Indiya ta amsa cewa Pakistan ta kakkaɓo jiragen yaƙinta

A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta amsa cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin artabunsu da ƙasar Pakistan

A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore.

Tun da farko, jami’an Indiya sun yi ta musanta duk wata asarar jiragen sama a cikin wannan arangama, wanda aka fara ne bayan wani hari da aka kai wa masu yawon bude ido a yankin Kashmir da Indiya ke mulka a watan Afrilu, wanda Indiya ta dora alhakinsa kan Pakistan.

Ita kuwa Pakistan, ta yi ikirarin cewa ta harbo jiragen Indiya da dama, ciki har da uku kirar Rafale na Faransa.

Lokacin da wani wakilin kafar yaɗa labarai ta Bloomberg ya tambaye shi kai tsaye game da iƙirarin Pakistan na harbo “jiragen Indiya shida,” Chauhan da farko ya musanta adadin a matsayin “cikakken kuskure.”

Amma daga baya ya canza zance, yana mai cewa, “abin da ke da muhimmanci shi ne dalilin da ya sa suka fadi,” yana nuni da cewa lallai an rasa wasu jiragen sama.

Bugu da ƙari, ya amince cewa sojojin Indiya sun yi “kuskuren dabara” a farkon fadan.

“Abin da ya yi kyau shi ne mun sami damar fahimtar kuskuren da muka yi, muka gyara, kuma muka sake aiwatar da shi bayan kwana biyu, muna sake kai hari daga nesa,” in ji Chauhan, yana mai nuna saurin daidaita dabarun bayan koma bayan na farko.

Faɗan na watan Mayu, wanda Indiya ta fara kai hare-hare a yankin da Pakistan ke iko da shi, ya nuna wani babban tashin hankali tsakanin kasashen biyu masu makamin nukiliya.

Daga ƙarshe an sanar da tsagaita wuta a ranar 10 ga Mayu, wanda ya kawo ƙarshen fadan na kwanaki hudu.