Yaƙi ya ɓarke tsakanin Indiya da Pakistan yayin da a safiyar wannan Larabar ƙasashen biyu suka riƙa yi wa juna musayar wuta da manyan makaman atilari.
Hakan na zuwa ne bayan harin da Indiya ƙaddamar kan Islamabad da sassafe, lamarin da ke nuna ɓarkewar rikici tsakanin maƙwaftan biyu masu makaman nukiliya.
- Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
- Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi
Indiya ta ce ta ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a kan wurare cikin Pakistan, a matsayin ramuwar-gayya ta harin da wasu ’yan bindiga suka kai yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikonta a watan da ya gabata — wanda a lokacin aka kashe fararen hula 26.
Kafafen yaɗa labarai na Pakistan sun bayar da rahoton jerin fashe-fashe a wurare daban-daban ciki har da birnin Muzaffarabad, da har wutar lantarki ta ɗauke.
Mutane sun mutu a dukkan ɓangarorin, saboda a yayin da Pakistan ta ce harin Indiya ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla takwas, a nata ɓangaren, Indiya ta ce fararen hula 3 sun mutu a kusa da Kashmir sakamakon harba manyan makaman atilari da Pakistan ta yi.
Wani jami’in gwamnatin Indiya, Azhar Majid ya ce Indiyawa 8 ne suka mutu, kana 29 suka samu rauni a wannan Laraba a garin Poonch na Kashmir, kusa da iyaka da Pakistan.
Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Asif ya ce an harbo jiragen yaƙin India biyar kuma an yi garkuwa da sojojin India takwas a matsayin fursunonin yaƙi.
Tun da farko, Ministan Watsa Labaran Pakistan Attaullah Tarar ya shaida wa TRT cewa an harbo jirgi guda ɗaya a birnin Akhnoor da ke yankin Kashmir wanda ake taƙaddama a kansa.
Sannan aka harbo wani jirgin a birnin Ambala na ƙasar Indiya, kazalika an harbo jirgi marasa matuƙi a lardin Jammu na ɓangaren Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya.
Tarar ya ƙara da cewa sojojin Pakistan sun mayar da martani ne kan harin da India ta kai ƙasar da makamai masu linzami waɗanda ta harba a yankunan “fararen-hula.”
Wani mai magana da yawun rundunar sojojin Pakistan ya ce sun “lalata” wasu kayayyakin tsaron India.
Indiya da Pakista sun sha gwabza faɗa tun bayan kafa su a shekarar 1947 da Turawan Birtaniya suka yi.