✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ango ya tsere tare da surukarsa

Rahul da mahaifiyarta suna tattaunawa ta waya sosai a cikin wata uku zuwa huɗu.

Ana zargin wani ɗan kasar Indiya mai shekara 20 da tserewa da surukarsa mai shekara 40, kwanaki tara kacal kafin aurensa da ’yarta.

Ma’auratan Rahul da Shibani, matasa ne ’yan Aligarh, a Jihar Uttar Pradesh ta Indiya, wadanda suka shirya yin aure a ranar 16 ga Afrilu na watan da muke ciki.

An aika wa dangi katin gayyata domin halartar taron bikin, amma kwanaki tara kafin ranar bikin, sai wani iftila’i ya afku.

Angon dan shekara 20 ya lallaba ya bace, amma bai tafi shi kadai ba; ya tsere da Anita, mahaifiyar amaryarsa mai shekara 40.

Domin munin lamarin, Angon da Anita sun kwashe kudaden ajiyar ma’auratan da kuma ajiyar dangin Anita, inda suka tatuke Shibani (amarya) da mahaifinta.

A ranar Lahadi 6 ga Afrilu, Rahul ya bar gidansu, yana mai cewa zai yi siyayya kayan biki.

Da daddare sai ya kira mahaifinsa ya shaida masa cewa, zai yi tafiya, amma kada ya damu da neman sa.

Kusan lokaci guda, Shibani ta lura cewa, mahaifiyarta da kudin ajiyarsu sun bace, sai dai ba ta bar wani sako ba.

Kodayake Shibani da mahaifinta mai suna Kumar sun lura da dangantakar da ba a saba ba gani ba a tsakanin Rahul da Anita, amma ba su ce komai ba, saboda ba sa son lalata auren.

“Ya kamata mu yi aure da Rahul a ranar 16 ga Afrilu, kuma mahaifiyata ta tafi tare da shi ranar Lahadi.

“Rahul da mahaifiyata sun kasance suna tattaunawa ta waya sosai a cikin wata uku zuwa huɗu,” kamar yadda Shibani ta shaida wa manema labarai na Indiya.

“Mahaifiyata ta kwashe duk kudinmu na shagalin bikin. Za ta iya yin dauk abin da take so yanzu, ba mu damu ba. Abin da muke so shi ne a mayar mana da kudinmu da kayan ado.”

Mijin Anita, Kumar yana sana’a ce a Bengaluru kuma yawanci ba ya zama, inda shi ma ya lura cewa Rahul ya fi yin magana da matarsa fiye da yadda yake yi da ‘yarsa.

Duk da haka, bai ce komai ba domin ranar biki ta kusa, kuma ba ya son bata abubuwa.

Ya shigar da karar wanda zai auri ’yarsa da matsarsa da suka bace da fatan ‘yan sanda za su iya gano su.

“Na kira Anita sau da yawa, amma ta kashe wayarta, na kuma kira mutumin da suke tare, amma ya ci gaba da musanta cewa ba ta tare da shi,” in ji Kumar.

Ya ce, “Wannan mutumin ba ya yin waya da ‘yata, said ai ya yi da matata,” in ji mahaifin Shibani.

“Ina zaune a Bengaluru don gudanar da kasuwancina, sai na ji cewa, tsawon wata uku da suka wuce, suna tattaunawa da juna na tsawon sa’o’i 22 a rana, na yi shakku, amma ban ce komai ba saboda an kusa daurin auren.

Anita ta tsare da mutumin a ranar 6 ga Afrilu kuma ta kwashe duk kudinmu da kayan ado.