✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Donald Trump ya taya ƙasashen biyu murna a kan amfani da hankalinsu da kuma basira.

Kasashen Indiya da Pakistan sun tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan shafe kwanaki suna yi wa juna luguden wuta da makaman atilare.

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da cewa ƙasashen biyu maƙwabta sun amince su cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta nan take bayan shafe dare guda ana tattaunawa.

“Bayan doguwar tattaunawa da Amurka ta yi na a cikin dare, ina farin cikin sanar da cewa Indiya da Pakistan sun amince da tsagaita wuta cikin gaggawa.

“Ina taya ƙasashen biyu murna a kan amfani da hankalinsu da kuma basira,” kamar yadda Trump ɗin ya bayyana a shafinsa na Truth Social.

Shi ma Ministan Harkokin Wajen Pakistan Ishaq Dar ya tabbatar da maganar Trump ɗin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce “Pakistan da Indiya sun amince da tsagaita wuta da gaggawa. Pakistan a ko da yaushe tana kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, ba tare da ƙasa a gwiwa kan ƙarfin ikonta da maratabar ƙasarta ba!

Ita ma Ma’aikatar Harkokin Wajen Indiya ta tabbatar da batun tsagaita wutar inda ta ce yarjejeniyar za ta fara aiki ne a ranar Asabar da misalin 1700 agogon Istanbul.