✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Ta’aziyyar Shugaban Sojin Kasa Bayan Harin Mauludi

Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja ya gana da al'ummar yankin Tudun Biri, inda harin kuskuren jirgin rundunarsa ya kashe mutum 85 a wurin Mauludi

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagba ya kai ziyarar ta’aziyya kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna, domin jajanta wa al’ummar kan harin jirgin rundunar da ya kashe mutane 85 a taron bikin Mauludi.

Wasu mutane 66 sun jikka a sakamkon hare-haren bom guda biyu da jirgi mara matuki na rundunar ya kai wa taron Mauludin a daren Lahadi.

A lokacin ziyar ta’aziyyar Laftanar-Janar ya shaida wa al’ummar cewa ba bisa ganganci aka kai harin ba, tsautsayi ne, ya kuma yi addu’ar Rahamar Allah ta kai ga mamatan.

Ga yadda ziyarar ta kasance: