✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke hukuncin rataya ga sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga sojan da ya kashe fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Goni Aisami.

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga sojan da ya kashe fitaccen malamin Musulunci a Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.

Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zama a garin Potiskum, ta yanke wa korarren sojan, Las Kofur John Gabriel hukuncin rataya ne a ranar Talata.

Alkalin kotun, Usman Zanna Mohammed, ya kuma yanke wa abokin lafinsa, Las Kofur Adamu Gideon, hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari.

Mai shari’a Usman Zanna Mohammed ya yanke wa Gabriel hukuncin ne karkashin dokar soja.

Sojan ta za a rataye yana aiki ne da bataliya ta 241 Recce da ke Nguru.

Shi kuma Gideon da ake yanke wa daurin shekaru 10 an same shi ne da laifukan hadin baki.

Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Mohammed ya ce bayan yin nazari sosai kan hujjojin da ke gaban kotun da kuma yadda wadanda ake tuhumar suka kasa bayar da wasu muhimman shaidu da za su tabbatar da da’awarsu, ya yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin da ya dace da su.

John Gabriel ya kashe  Sheikh Goni Aisami ne bayan malamin ya dauke shi a mota domin rage masa hanya a Karamar Hukumar Karasuwa ta jihar Yobe.

A kokarinsa na kwace motar malamin ya harbe malamin sau biyu, a kan hanyarsa ta zuwa Gashua daga Kano a ranar 22 ga watan Agustan 2022.

Daga bisani Gideon ya zo wajen domin taimkon sa su tafi da motar, amma dubunsu ta cika.

Sakamakon haka, gwamnatin jihar Yobe ta hannun ma’aikatar shari’a ta kai kara kotu wanda ya kai ga yanke hukunci a ranar wannan Talata 5 ga Disamba, 2023.