Wani mummunan hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da mata 10 a jihar Kebbi wadanda tuni suka riga mu gidan gaskiya.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kebbi (SEMA), ta ce ana tsammanin mai yankar kauna ta yi wa mata goma lullubi ne a sanadiyar kifewar kwale-kwale a tsakiyar kogi a Karamar Hukumar Jega ta jihar.
Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Sani Dadodo, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai.
Ya ce tsautsayi ya rutsa da matan yayin da a ranar Litinin suka tashi daga kauyen Gehuru zuwa wani kauyen da ke tsallaken kogi domin halartar shagalin biki.
Lamarin ya auku ne yayin da igiyar ruwa ta kifar da kwalekwalen da matan ke ciki wanda hakan ya yi sanadiyar dulmiyewarsu.
Alhaji Dododo ya ce gwanayen ninkaya sun gano gawar hudu daga cikin matan yayin da aka bazama wajen neman ragowar shidan daga fadama zuwa fadama.
Ya alakanta aukuwar iftila’in da ambaliyar ruwa wadda ta shafi kusan dukkan fadin jihar sakamakon mamakon ruwan sama da ke sauka, lamarin da ya sa koguna suka cika makil.
Ya kara da cewa, matukin kwalekwalen da aka kera da katako shi ne kadai ya tsallake rijiya da baya.