✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci gwamnatin Kano ta dabbaka dokar tattalin arzikin mata a jihar

An bukaci gwamnatin jihar Kano da ta dabbaka dokar tattalin arzikin mata ta kasa (WEE) domin inganta da rayuwar mata da habaka tattalin arzikinsu a…

An bukaci gwamnatin jihar Kano da ta dabbaka dokar tattalin arzikin mata ta kasa (WEE) domin inganta da rayuwar mata da habaka tattalin arzikinsu a jihar.

Shugabar kungiyar nan mai zaman kanta ta Isa Wali Empowerment Initiative (IWEI), Hajiya Amina Hanga ce ta yi kiran a ranar Talata yayin wani taron wakoki kan tattalin arzikin mata da kungiyarta ta shirya a wani bangare na bikin Ranar Yara ta Duniya ta 2025.

Ta ce an shirya taron ne a ranar ta yara inda yara dalibai musamman mata suka yi bajekolin fasaharsu ta waka a kan maudu’in tattalin arzikin mata.

A cewar shugabar, “Dokar Tattalin Arziki ta Mata ta Kasa (WEE) wani daftari ne da ya kunshi alkiblar Najeriya kan bunkasa harkokin tattalin arzikin mata da inganta hanyoyin samun kudadensu. Dokar tana kokarin ganin an rage gibin da ke tsakanin maza da mata ta bangaren samun kudaden shiga, ilimi da kuma aiki yi ta yadda za a habaka tattalin arzikin kasa.

“Dokar ta fayyace hanyoyin da za a bi a fannoni daban-daban wajen ganin ba a bar mata a baya ba a harkar dogaro da kai. Muna kuma hada gwiwa da Ma’aikatar Harkokin Mata ta nan Kano domin ganin an dabbaka dokar a nan jihar.

“Mun zabi yin gasa a kan wakoki ne saboda hanya ce mai tasiri da wasu ke amfani da ita wajen isar da sako ga jama’a musamman matasa.

“Dama ce da muke amfani da ita wajen wayar da kai a kan dogaro da kai na mata. Wata hanya ce da muke amfani da ita wajen nusar da mata cewa za su iya zama masu dogaro da kansu ba tare da sun jira gwamnati ba,” in ji Amina Hanga.

Ita ma a nata bangaren, fitacciyar marubuciyar nan wacce kuma ita ta jagoranci alkalan da suka yi hukunci kan daliban da suka fafata a gasar, Nasiba Babale, ta ce gasar wata kyakkyawar hanya ce ta isar da sako ga daliban.

Nasiba, wacce kuma ita ce Daraktar Kirkira a kungiyar marubuta wakoki ta Poetic Wednesdays, ta ce, “Waka ta wuce hanyar nishadantar da jama’a ko kuma hanyar rubutu kawai, wani abu ne da yake taba zuciya kai tsaye. Mutane sukan fi mayar da hankali su saurari sakonka ta hanyoyi irin su waka, fiye da a ce kawai magana kake musu kai tsaye kamar kana karantawa daga littafi. Wannan ne ma ya sa muka yi amannar cewa amfani da waka domin isar da sakon zai yi tasiri sosai.”

Bayan fafatawa a gasar, daliba Rahama Ishaq daga Makarantar Sakandaren Gwamnati ta ’Yan Mata da ke Hausawa, wato GGSS Hausawa ce ta zo ta daya, inda ta samu kyauta tare da sauran wadanda suka yi kokari har zuwa matsayi na hudu.