Wasu ƙungiyoyin mata a ƙauyukan Bendeghe-Ekiem da Abiya da ke Ƙaramar Hukumar Etung, a Jihar Kuros Riba, sun yi barazanar gudanar da zanga-zangar tsirara idan gwamnati ba ta janye ƙudirin sayar da gonakin koko ba.
Matan sun ce wannan shawara da gwamnati ta ɗauka ba su aminta da ita ba, domin gonakin koko su ne tushen rayuwarsu, wanda da su suke cin abinci, suke biya wa ’ya’yansu kuɗin makaranta.
Aminiya ta samu rahoton cewa gwamnati na shirin sayar da hannun jarinta a wasu manyan gonakin koko da ke wannan yanki, wanda hakan ya fusata matan da sauran al’ummar ƙauyukan da abin ya shafa.
Majiyarmu ta ce, “Idan gwamnati ta sayar da hannun jarinta, to tamkar hana mu cin moriyar aikin gonarmu ne. Wannan mataki ya saɓa wa yarjejeniyar da aka taɓa yi a baya.”
A ƙarshen mako, wasu daga cikin matan sun gudanar da zanga-zanga r lumana don nuna rashin amincewarsu da wannan ƙudiri.
Sai dai duk da ƙoƙarin sasanci daga Ma’aikatar Ayyukan Gona ta jihar, matan sun bai wa gwamnati wa’adin mako biyu ta janye shirin, ko kuma su fito su yi zanga-zangar tsirara.
Shugabannin ƙungiyoyin matan; Ntunkai Mary Obi da Cif Helen Ogar, sun roƙi Kwamishinan Ayyukan Gona, Johnson Ebokpo, da ya kai wa gwamnan kokensu, domin a samu mafita kan lamarin.
“Mun bai wa gwamnati mako biyu ta janye wannan ƙudiri ko kuma a zauna da shugabanninmu domin a cimma matsaya.”
Baya ga matan, wasu shugabannin matasa da dattawan yankin irin su Kwamared Tandu Kingsley da Mista Etta Atu-Ojua, sun goya matan baya.
Sun ce: “Idan gwamnati ta sayar da gonakin, matasa ba za su ƙara samun abin yi ba, kuma hakan zai jefa wasu cikin ayyukan daba da sata.”
Sun buƙaci gwamnatin ta sake nazari da idon basira, domin kada al’umma su shiga cikin ƙalubalen rayuwa.