Hukumar Kula da Yanayi (NiMet), ta sake fitar da gargaɗi game da yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin a daminar bana.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta bayyana cewa Jihar Akwa Ibom ce ke fuskantar barazana mafi tsanani a halin yanzu.
- Gwamnan Kaduna ya bai wa sabon Sarkin Moro’a sandar mulki
- Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a Iran
Sauran jihohin da abin ka iya shafa sun haɗa da Sakkwato, Zamfara, Filato, Yobe, Bauchi, Bayelsa, Nasarawa, Binuwai, Ogun, Ekiti, Delta da kuma Ribas.
NiMet ta shawarci al’umma, musamman waɗanda ke zaune a cikin waɗannan jihohin, da su tabbatar sun yashe magudanan ruwa domin bai wa ruwa hanyar wucewa.
Haka kuma ta buƙaci mutane da su nisanci wuraren da ke da hatsarin ambaliya, kuma idan ruwa ya fara ƙarfi, su bar irin waɗannan wuraren domin kare lafiyarsu.
Ambaliya dai na daga cikin manyan matsalolin da ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi a Najeriya a duk shekara.
A makonnin baya, garin Mokwa da ke Jihar Neja ya fuskanci ambaliya wadda ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 230.