✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet

A ranar Laraba da safe kuma, za a samu iska mai ƙarfi da ruwa a Katsina da Kano da Bauchi da Sakkwato da Taraba.

Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta sanar da cewa a ’yan kwanakin nan za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a wasu jihohi da ke sassa daban-daban na ƙasar.

Hakan na kunshe cikin hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025 da hukumar ta fitar.

NiMet ta shawarci al’umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa.

A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za su fuskanci iska mai ƙarfi haɗe da ruwan sama.

Hasashen ya nuna cewa a ranar Litinin da safe, an samu ruwan sama da iska a jihohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Sakkwato da Kaduna.

Ya kuma nuna cewa yankin tsakiyar kasar kamar Abuja da Neja da Filato da Nasarawa da Benuwe da Kogi su ma za su samu ruwan sama daga rana zuwa yamma.

Ranar Talata da safe kuma ana sa ran ruwan sama da tsakar rana a Abuja da Kwara da Neja da Filato.

A ranar Laraba da safe kuma, za a samu iska mai ƙarfi da ruwa a Katsina da Kano da Bauchi da Sakkwato da Taraba sannan daga baya za a samu a Yobe da Jigawa da Kaduna da Borno da kuma Kebbi.