✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya jajanta wa al’ummar Garin Kestu da ke unguwar Atuwo a ƙaramar hukumar Shanga a jihar.

Guguwar ruwan sama ya lalata gidaje da dama a ƙaramar hukumar Shanga ta Jihar Kebbi.

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya jajanta wa al’ummar Garin Kestu da ke unguwar Atuwo a Ƙaramar hukumar Shanga, ya kuma buƙaci iyalan waɗanda abin ya shafa da su ɗauki lamarin a matsayin wata ƙaddara.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Ahmed Idris ya fitar.

A cewar sanarwar, gwamnan wanda shugaban Ƙaramar hukumar Shanga, Audu Audu ya wakilta, ya ce ruwan sama mai ƙarfi da ya afku a daren ranar Talata ya lalata gidaje da dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Ya kuma tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa, gwamnati za ta bayar da tallafi da suka haɗa da kayayyakin gini.

Gwamnan ya kuma buƙace su da su yi haƙuri, inda ya yi alƙawarin cewa nan ba da daɗewa ba gwamnatin jihar za ta kawo musu ɗauki.