Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM), sun fara aikin tantance ɓarnar da ambaliya da iska suka yi a yankunan Kudancin Kaduna.
Manufar aikin ita ce su tattara sahihan bayanai daga jama’a da shugabanninsu domin a samu taimako da kuma tsara hanyoyin kare aukuwar hakan a gaba.
- Sabon harin Iran ya hallaka mana mutum 8 – Isra’ila
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba
Yayin da suka kai ziyara Ƙaramar Hukumar Jama’a, Ko’odinetan KADSEMA na Kudancin Kaduna, Mista Ayyuka Shemang, ya ce sun fara wannan aiki ne saboda hasashen ambaliya daga Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMet).
Ya jaddada muhimmancin shirye-shirye tun kafin saukar daminar bana.
Shugaban tawagar IOM a Kaduna, Arhyel Mbaya, ya ce wannan aiki yana da muhimmanci don a tabbatar da cewa waɗanda ambaliya da iska suka shafa sun samu taimako yadda ya kamata.
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Jama’a, Emmanuel Moses Utung, ya yaba da aikin, inda ya ce sun riga sun umarci kansiloli su tattara bayanai daga mazaɓunsu.
Tawagar ta haɗa da wakilai daga Red Cross, kafafen watsa labarai, ƙungiyoyin addini, sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati.
Waɗannan na taimakawa wajen tabbatar da cewa an gano duk wuraren da abin ya shafa.
Ana sa ran bayanan da za a samu daga wannan aiki za su taimaka wajen tsara agajin gaggawa da kuma shirye-shiryen don tunkarar sauyin yanayi a Kudancin Kaduna.