Tsafta tana kasancewa wani muhimmin ɓangare na rayuwar mace. Duk da cewa galibi ana alaƙanta tsafta da kyawun gani ko ƙamshi, sai dai a zahirin gaskiya tsafta ta wuce gaban haka.
Ita ce turbar zaman lafiya a gidan aure, makamin janyo soyayya, da ginshiƙin lafiyar jiki da tunani.
- Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya
- Gwamnatin Kano ta haramta ‘Ƙauyawa Day’ a lokacin bikin aure
Wasu matan na iya cika ido da kwalliya a wajen biki ko taro, amma su kan bar gidansu cikin ƙazanta da rashin tsafta. A wasu lokuta kuma, akwai matan da rashin tsaftarsu ke janyo mutuwar aurensu, rashin kulawa da miji, ko kuma sa mijin ya ɗauki matakin ƙaro aure.
Tsafta na nufin gyara da killace jiki, gida da muhalli daga datti da duk wani abu da zai iya haifar da wari, cuta ko gurɓata. Tsafta ba wai gyaran jiki kawai ba ce, tana shafar jikinmu, tunaninmu, lafiyarmu da zamantakewarmu.
Kamar yadda wani tsohon karin magana ke cewa, “namiji ƙazami ba ya dawwama da matar tsafta”. A nan za mu fahimci cewa idan mace na da tsafta da ladabi, hatta ɗabi’ar mijinta na iya sauyawa.
Nau’o’in ƙazanta a tsakanin matan aure
Kamar yadda ake da mata masu tsafta, akwai nau’o’i daban-daban na matan da rashin tsafta ya yi wa ƙatutu. Ga wasu nau’o’in da ke da illa sosai ga zaman aure:
1. Ƙazama ta farko:
Ita ce wadda za ka ganta cikin ado da kwalliya a wajen taro, riga ɗauke da ado tsaf, humra da turare, har mutum na iya tsoron kusanci da ita saboda kyan gani. Amma idan Allah Ya kai ka gidanta, sai ka ruɗe: tsakar ga datti, ɗaki da kicin cikin wari da ɗaukar hankali. Wannan na nuni da cewa ado ba yana nufin tsafta ba.
2. Ƙazama ta jiki:
Wannan ita ce wadda ko uwa ba za ta so zama kusa da ita ba. Hammata da gaɓoɓin jiki duk sun cika da wari. Rashin wanka akai-akai, rashin amfani da turare ko sabulu mai ƙamshi, duk sun zame mata jiki. A nan, har mijinta zai iya ɗaukan matakin ƙin kusantarta ko ya bar mata gidan gaba ɗaya.
3. Kazama ta zuciya da muhalli:
Wannan ita ce mafi hatsari. Ba wai kawai jiki da gida ne suke kasancewa cikin ƙazanta ba, har zuciyarta cike take da gori, tsegumi, rashin ladabi da yawan shiga rayuwar wasu. Gidanta tamkar filin yaƙi yake, yara na yawo da datti, kayan wanki a kowane lungu, ko da dare ko rana babu bambanci. Wannan mace ce da har zuciyarta ba ta son tsafta.
Illar ƙazanta a zaman aure
Ƙazanta tana haifar da matsaloli da dama a gidan aure, kamar haka:
- Rage sha’awa da kusanci tsakanin ma’aurata.
- Hana mijin jin daɗin zaman gida.
- Sa mijin yanke hukuncin ƙaro mata ko ficewa daga gidan gaba ɗaya.
- Ƙara zaman ƙunci da rashin nishaɗi.
- Sa yara su taso cikin halin rashin tsafta da sakaci.
Akwai karance-karance da dama da ke tabbatar da cewa tsafta tana rage yiwuwar kamuwa da cututtuka irin su cututtuka masu yaɗuwa, UTI, ko ma zazzabin taifod da ya kan faru sakamakon rayuwa cikin datti.
Muhimmancin tsafta ga mace a gida
- Tsafta na ƙara daraja da martabar mace a idon mijinta da al’umma.
- Tana sa yara su taso cikin kyawawan ɗabi’u.
- Tana ƙara jin dadi da soyayya a tsakanin miji da mata.
- Ita ce ginshiƙin lafiya da nishaɗi a gidan aure.
Gargaɗi da tuni
’Yan uwana mata, a yau mace ce ginshiƙin gidanta. Tsaftace jiki, muhalli da zuciya na daga cikin nauyin da ya rataya a kanmu. Idan kin bar kanki cikin halin ƙazanta, ki sani ba mijinki kaɗai za ki sa a wahala ba, har da yaranki da kuma makomar zamantakewarsu.
Ki duba a yau, idan ke ce ke yawan zagi, gori da shisshigi, ko ke ce ke yawan barin gida cikin datti, ki gyara kafin a kai ga faduwa ƙasa babu nauyi. Ka da ki zamo uwa wadda ’yarta ke jin kunya a faɗi cewa ke ce mahaifiyarta.
Tsafta alamar tarbiyya ce, tsafta alamar soyayya ce, kuma tsafta alamar lafiya ce. Idan har muna son zaman lafiya da jin daɗi a gidanmu, musamman a tsakanin ma’aurata, to lallai tsafta ce gaɓar farko da ya kamata mu tsaya mu gyara. Idan kunne ya ji, gangar jiki ta tsira.
“Tsafta na daga cikin sirrin ɗorewar soyayya da martaba a gidan aure.”