✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da fasinjoji ke ciki bayan hatsarin jirgin sama a Ilori

Hukumar NSIB ta gano katin nadar bayanan jirgin horon kwalejin koyon tukin jirgi da ya yi hatsari a Ilori

Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya (NSIB) ta sanar cewa mutanen da suka tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgin sama da ya auku a Jihar Kwara suna samun kulawa a asibiti

Da yake tabbatar da cewe duka mutanen cikin jirgin horon sun tsira da ransu, Babban Daraktan NSIB, Kyaftin Alex Badeh Junior, ya ce hukumar ta gano katin nadar bayanai daga jirgin, bayan aukuwar hatsarin a filin jirgin sama na Janar Tunde Idiagbon da ke Ilorin,

Jirgin, nau’in Diamond, mai lamba BNI, mallakin Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama ta Ilorin (IAC) ne, kuma ya yi hatsarin ne a yayin atisayen sauka na gwaji, inda ya kauce daga titi, ya yi cikin daji ya lalace fiye da yadda za a iya gyarawa.

Kyaftin Badeh ya bayyana Ya ce wadanda ya yi hatsari da su sun hada da shugaban horo, wanda aka sani da Ajape, da wata daliba, Lola. Dayansu ya samu rauni mai tsanani, ɗayan kuma ya samu raunuka marasa yawa, kuma dukansu suna karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH).

Ya bayyana cewa ana nazarin katin bayanan da aka gano a dakin gwaje-gwajen NSIB, kuma ana sa ran za a fitar da rahoton farko cikin kwanaki 30 masu zuwa.

Ya jaddada cewa aikin hukumar shi ne gano abin da ya faru da kuma yadda za a hana sake faruwar irinsa a nan gaba, yana mai tabbatar wa jama’a cewa duk da hatsarin da ya faru, sararin samaniyar Najeriya yana nan cikin aminci.