✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kai ƙarar kamfanin jirgi da fasinja kan kukan yaro

Matar ’yar kasar Brazil da ta ki barin kujerar kusa da taga saboda wani yaro mai kuka ta shigar da kara a kotu.

Wata mata mai suna Jennifer Castro ta shigar da ƙarar kamfanin jiragen sama na GOL da wata fasinja a kotu bisa wani faifan bidiyo aka wallafa da yake nuna matar ta ki barin kujerarta da ke kusa da taga saboda wani yaro da yake kuka.

Matar ’yar ƙasar Brazil da ta ƙi barin kujerar kusa da taga saboda wani yaro mai kuka ta shigar da ƙara a kotu.

Jennifer Castro, mai shekara 29 na daukar matakin shari’a a kan kamfanin jiragin sama na GOl da kuma fasinjar da ta ɗauki bidiyonta a lokacin da lamarin ya faru.

Lamarin wanda aka yi ta yadawa ta intanet, ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.

A cewar jaridar The New York Post, Castro na tuhumar kamfanin jirgin da kuma matar da ya nadi musayar takaddamar da suka yi, inda ta nemi diyya kan halin kunci da barnar da lamarin ya haifar mata.

Ta bayyana cewa, matakin da ta ɗauka na shigar da ƙarar shi ne don hana afkuwar irin wannan abin kunya ga jama’a a nan gaba.

Al’amarin ya ja hankalin jama’a saboda yada lamarin a kafafen sada zumunta.

Da take bayani a kan shari’ar, Castro ta ki bayyana adadin diyyar da take nema.

Ta ce, tana son hana irin wannan tozarta jama’a da abin da ta kira fallasa ba tare da izini ba a nan gaba.

Hakan na zuwa ne bayan da aka bayar da rahoton cewa, a watan da ya gabata ta fara “tunanin” daukar matakin shari’a.

Castro ta bayyana cewa, “tun bayan faruwar wannan lamarin, rayuwata ta shiga wani yanayi da ban taba tunanin sa ba.”

“Abin da ya kamata ya kasance kawai jirgin zirgazirgar na yau da kullun ya sauya zuwa wani abun kunya, yana fallasa ni da rashin adalci da haifar da sakamakon da ya shafi rayuwata ta sirri da ta sana’a.

Ni ce ake so na yanke hukunci a kan takaddama da hasashen mutanen da ba su ma san cikakken labarin ba.”

Castro ta ce lamarin ya fara ne a lokacin da take hawa jirgi, sai ta hangi wani yaro a zaune a lambar kujerar da ya kamata ta zauna.

Tunda ta riga ta zabi wurin zama na kusa da taga, Castro ta yi tsammanin yaron zai koma wani wurin zaman na daban.

“Na jira shi yadda ya kamata, amma ya kwantar da kansa a wata kujerar, sannan sai na zauna a kujerata ,” in ji ta.

Lamarin ya ta’azzara lokacin da wata ta fara daukar bidiyon Castro ba tare da izininta ba.