Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya.
Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47.
- Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu
- Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa.
Sanarwar ta ce “a ranar Lahadi 15 ga watan Yuni, dan gidan wani jami’in dan sanda mai kimanin shekara goma da haihuwa ya harbe mahaifinsa har lahira ya kuma jiwa yayan sa mummunan rauni.
“Abin bakin ciki muna sanar da ku mutuwar jami’inmu mai mukamin sufeto, Okolie Amechi, bisa harbe shi da dansa ya yi a gidansa.
“Wannan ba karamin abin takaici ba ne da kaddara,” in ji sanarwar.