✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a Sakkwato

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ƙananan yara sun nemi a yi wa yaron da aka kashe adalci.

An shiga ruɗani a unguwar CBN Quarters da ke cikin birnin Sakkwato, inda wani ƙaramin yaro ɗan shekara huɗu mai suna Ayman Abubakar, ya ɓace, amma daga bisani aka gano gawarsa a cikin ramin sokawe.

Ana zargin wani maƙwabcin iyayen yaron da wata mata da aikata wannan ɗanyen aiki.

Ƙngiyoyi da ke fafutukar kare haƙƙin yara da martabar bil adama sun bayyana wannan kisa a matsayin babban cin zarafi.

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, shugaban NACTAL na ƙasa Abdulganiyu Abubakar, Usman Ahmad daga ƙungiyar kare haƙƙin yara, da Rabi’u Bello Gandi shugaban hukumar kare cin zarafin jinsi, sun yi Allah-wadai da kisan yaron.

“Kashe wannan ƙaramin yaro cin zarafi ne na keta haƙƙin ɗan Adam, kuma lamarin da ya saɓa da doka.

“Wannan mummunan abu ne da ke ƙara nuna irin haɗuran da yara ke fuskanta a cikin al’umma.”

Ƙungiyoyin sun buƙaci a gudanar da bincike don gano gaskiya tare da ɗaukar matakin hukunta duk wanda ke da hannu a kisan.

“Muna kira da a tabbatar da an yi gaskiya da adalci, a kuma hukunta waɗanda ke da hannu a kisan Ayman. Hakazalika, ya zama dole a riƙa bayyana wa jama’a irin ci gaban da ake samu a yayin bincike lokaci bayan lokaci.”

Sun jaddada buƙatar a ɗauki matakan gaggawa na kare yara daga faɗa wa hannun miyagu.

“Kare haƙƙin yaron ɗan Najeriya lamari ne da ya kamata a bai wa fifiko a ƙasa, a daina wasa da shi.”

Mahaifin Ayman, Dakta Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan yadda lamarin ya faru.

“Na rasa ɗana ne ranar 29 ga watan Maris, bayan ya dawo daga sallar La’asar. Mun yi ta nemansa har tsawon sati bakwai ba tare da nasara ba. Daga baya sai aka gano gawarsa a cikin ramin sokawe.”

Ya roƙi al’umma su mara masa baya wajen ganin an yi wa ɗansa adalci.

Rundunar ’yan sandan jihar, tabbatar da cewa ta kama waɗanda ake zargi, kuma an fara gudanar da bincike a kansu.

Ƙungiyoyin sun yi alƙawarin ganin cewa sun bibiyu lamarin don tabbatar da gaskiya da adalci.

“Za mu tsaya tare da iyayen Ayman domin tabbatar da cewa an yi adalci. Adalci ga Ayman, adalci ne ga kowa.”