✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok

’Yan ta’addan sun buɗe wa mutanen wuta ne a yayin da suke shirin gudanar da addu'o'i ga ’yan uwansu da suka rasu

Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe masu zaman makoki bakwai tare da jikkata wasu a ƙauyen Kopl da ke Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.

Shugaban Karamar Hukumar, Honorabul Modu Mustapha, ya ce mayaƙan sun buɗe wa mutanen wuta ne a yammacin ranar Litinin, a yayin da suke shirin gudanar da addu’o’i ga ’yan uwansu da suka rasu.

Ya ce, “Sun taru ne domin yin addu’a lokacin da ’yan ta’addan suka sauka a kansu. Mun kwashe mutane da yawa da suka samu raunukan harsashi zuwa Babban Asibitin Mubi da ke maƙwabtaka da Jihar Adamawa.

“Adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, saboda wasu sun tsere cikin daji da raunukan harsashi. Ana ci gaba da aikin nemowa da ceto waɗanda ke cikin daji,” in ji shi.

Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ci gaba da yin Allah wadai da hare-haren, inda ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin da ya wuce tunanin dan Adam.

“Ko jiya ma, na samu kiran gaggawa cewa an kashe sama da ’yan banga 10 a wani yankin da ke tsakanin Karamar Hukumar Hawul ta Jihar Borno da garin Garkida a Jihar Adamawa.

“Al’ummata na fama da munanan asara ba tare da wani faɗa ba. A cikin wata guda da ya gabata kaɗai, an kashe sama da mutum dari a hare-hare da dama yankunan Sabon Gari da Izge da Kirawa da Pulka da Damboada Chibok da Askira Uba da wasu da yawa da ba zan iya lissafawa ba,” in ji Sanata Ndume.