✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe

Ana zargin cewa mahaifin yaron shi ne jagoran kisan kuma Yana cikin waɗanda suka tsere

Wani mummunan al’amari ya girgiza al’umma a Ƙaramar Hukumar Kwami, Jihar Gombe, inda ake zargin wani magidanci ya jagoranci sacewa da kashe ɗansa mai shekara shida domin yin tsafin kuɗi.

Ana zargin cewa mahaifin yaron shi ne jagoran kisan kuma Yana cikin waɗanda suka tsere, a yayin da hukumomi ke ci gaba da farautar sa.

Tuni ’yan sanda suka cafke mutane takwas bisa zargin wannan aika-aika a unguwar Bura-Bunga da ke ƙaramar hukumar.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya sanar cewa waɗanda suka shiga hannu sun amsa cewa sun kashe yaron ne bisa umarnin bokaye da suka nemi sassan jikin ɗan Adam don yin tsafin kuɗi.

Bincike ya nuna wani mai shekaru 45, wanda ake zargin shi ne shugaban gungun, ya hallaka yaron tare da raba sassan jikinsa gida biyu.

Ɓangaren sama na jikinsa an jefa shi cikin rijiyar, yayin da ɓangaren kasa aka bai wa abokan laifinsa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu bokaye biyu ne suka nemi sassan jikin yaron, kuma wani matashi mai shekaru 18 ne ya sace yaron, sannan wani ya haɗa bokayen da su.

Kwamishinan ’yan sanda, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa za a tabbatar an gurfanar da duk masu hannu a wannan mummunan kisa a gaban ƙuliya.

Ya kuma yi kira ga jama’a su riƙa sa ido tare da bayar da rahoto kan duk wani abu mai kama da waɗanda ake nema jami’an tsaro.

Rundunar ’yan sanda ta jaddada aniyarta na kawo ƙarshen irin waɗannan munanan laifuka a faɗin jihar ta Gombe.