Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dokta Abdullahi Ganduje ya yi alhinin rasuwar darakta a masana’antar Kannywood Aminu Surajo Bono.
Aminiya ta ruwaito cewa, Aminu S. Bono ya rasu ne da yammacin Litinin bayan ya yanke jiki ya fadi.
- HOTUNA: Yadda aka yi Janai’zar Daraktan Kannywood Aminu S Bono
- Daraktan Kannywood Aminu S Bono ya rasu
Cikin wata sanarwa da mai yada labaransa, Edwin Olofu, ya fitar ranar Talata, Dokta Ganduje ya ce ya kadu matuka bayan samu labarin rasuwar shahararren darakta.
Ganduje wanda ya ce rasuwar Darakta Aminu Surajo Bono babban gibi ne a masana’antar Kannywood.
Shugaban jam’iyyar ya kara da cewa Darakta Aminu Surajo Bono ya yi amfani da lokacinsa wajen bunkasa masana’antar Kannywood ta hanyar gudanar da tsaftatacciyar rayuwa.
Ganduje ya ce, “Na kadu matuka da samun labarin rasuwar Darakta Aminu Surajo Bono. Wannan ba rashi ba ne kawai ga masana’antar Kannywood ba, rashi ne ga al’umma.
“Ina amfani da wannan dama domin mika ta’aziyya ga iyalansa da ‘yan uwansa da masana’antar Kannywood. Ina rokon Allah Ya ba su juriyar wannan rashi.
“Tabbas rayuwar Darakta Aminu Surajo a cikin finafinai da kuma zahiri abar yabawa ce.”
Dokta Abdullahi Ganduje ya ce yana rokon Allah (SWT) Ya ba wa iyalansa da masana’antar Kannywood juriyar wannan babban rashi, yana mai rokon Ya gafarta wa mamacin.