✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: Yadda aka yi Janai’zar Daraktan Kannywood Aminu S Bono

Manyan ’yan Kannywood sauran al'umma sun yi cikar kwari wajen halartar Sallar Jana'izar fitaccen dan Kannywood, Aminu S. Bono a Kano.

A safiyar Talatar nan aka yi jana’izar fitaccen jarumi, darakta kuma mawakin Kannywood, Aminu S. Bono, wanda ya riga mu gidan gaskiya.

Manyan ’yan Kannywood sauran al’umma sun yi cikar kwari wajen halartar Sallar Jana’izar da aka gudanar a Filin ’Yar Mai Shinkafi da ke mahaifarsa a unguwar Dandago a birnin Kano.

Daga nan kuma aka wuce da shi zuwa makwancinsa na karshe a Makabartar Dandolo da ke unguwar Goron Dutse.

A yammacin ranar Litinin Allah Ya masa rasuwa a Kano, bayan ya yanke jiki ya fadi.

Ga hotunan yadda jana’izarsa ta kasance.

%d bloggers like this: