✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daraktan Kannywood Aminu S Bono ya rasu

Marigayi Aminu S. Bono ya rasu ne da yammacin Litinin bayan da ya yanke jiki ya fadi.

Allah Ya yi wa fitaccen darakta a masana’antar Kannywood Aminu S. Bono rasuwa.

Marigayi Aminu S. Bono ya rasu ne da yammacin Litinin bayan da ya yanke jiki ya fadi.

Aminu S. Bono daraktan finafinai ne da wakokin Kannywood ne, kuma haifaffen unguwar Dandago a cikin birnin Kano.

Ya yi firamare da sakandire a Kano, sannan ya fara fim a shekarar 1999.