Gwamnatin Faransa ta ce jakadanta zai fice daga Jamhuriyar Nijar nan ba da jimawa ba, sannan sojojinta da ke can su bi sahu daga watan Oktoba mai kamawa.
Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa, “Nan da sa’o’i kadan jakandanmu da sauran jami’an jakadancin Faransa da ke Nijar za su dawo gida.
- A gaggauta kuɓutar da sauran ɗaliban jami’ar da aka sace a Gusau — Tinubu
- NAJERIYA A YAU: “Yadda Na Sayar Da Gado Na Na Yi Karatu”
“Kawancen aikin sojin Faransa da Nijar ta kare, don haka cikin makonni masu zuwa sojojin Faransa za su fara barin Nijar, wanda za su kammala zuwa karshen shekara.”
Macron ya sanar da haka ne a wata hirar talabijin a ranar Lahadi, amma bai fayyace yadda janyewar sojojin za ta kasance ba.
Ya ce, masu juyin mulkin Nijar sun haramta wa jiragen kasarsa shawagi a sararin samaniyar kasarsu, amma duk da haka, “A ’yan makonni masu zuwa za mu tattaunda masu juyin mulkin Nijar, saboda muna so a yi komai cikin lumana.”
Daidai ke nan —Masu juyin mulki
Sabuwar gwamnatin sojin Nijar ta yi maraba da sanarwar ta Macron, a matsayin “babban abin tarihi da kuma kyakkyawan cigaba wajen tabbatar da ’yancin kasar Nijar da al’ummarta.”
Sanawar da gwamnatin, wadda ta hambarar da Shugaba Mohammed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli ta fitar ta kara da cewa, “Sojojin Faransa da jakadansu za su fice daga doron kasar Nijar nan da karshen shekarar nan.”
Tun lokacin da sojojin suka yi juyin mulki suka hakikance cewa dole dakarun Faransa da ma jakadanta su fice daga jihar.
Wannan na zuwa ne bayan zanga-zangar kin zaman dakarun Faransa ta yawaita a Nijar, tun bayan da sojoji suka yi wa na hannun damanta, Shugaba Mohamed Bazoum, juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli.
Faransa ta girkes sojojinta 1,500 a Nijar domin taimaka wa kasar yaki da masu ikirarin jihadi da suka addabi yankin Sahel da hare-haren ta’addanci.
Bayan juyin mulkin ne gwamnatin sojin Nijar ta ba wa Jakadan Faransa a kasar, Sylvain Itte, wa’adin awa 28 ya fice daga kasar, amma ya ce ba za ta za ta sabu ba, saboda gwamnatin kasar ba ta kallon sojojin a matsayin halastattun jagororin kasar.
A hirar da aka yi da Macron ranar Lahadi, ya jaddada cewa Bazoum da ke tsare a hannun sojojin shi ne ‘kadai halastaccen’ shugana ksar Nijar mai ci.
A cewarsa, tsarewar da aka yi wa jakadan kasarsa a cikin ofishin jakadancin da ke birnin Yamai, garkuwa da shi ne.
“Masu juyin mulkin sun nufe shi ne saboda yana aiwatar da sauye-sauye na gari ba tare da tsoro ba, lura da bambancin kabilanci da tsaro daga wasu ’yan siyasar kasar,” in ji Macron.
A baya-bayan nan sojoji sun sha yin juyin mulki a kasashen yankin Sahen inda suka zababbun shugabanni a kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da kuma Guinea.