Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Isa-Sabon Birni daga Jihar Sakkwato, Honorabul Abdulkadir Jelani Danbuga ya rasu.
Dan majalisa mai wakiltar Sabon Birni ta Kudu a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Aminu Almustapha (Boza) ya shaida wa wakilinmu cewa Honorabul Abdulkadir Jelani Danbuga ya saru ne bayan gajeriyar rashin lafia.
- An kama shi kan yunƙurin fyaɗe ga ’yar shekara 85
- Rikicin Gaza: Netanyahu na neman tayar da Yakin Duniya na Uku
Ya ce da farko an kwantar da marigayin a asibiti a ranar Talata, kafin Allah Ya yi masa cikawa da misalin 12.30 na dare.
Ya ce, “Za a kai shi Babban Masallacin Kasa da ke Abuja, inda za a yi masa wanka, sannan a kai shi Sakkwato a yi masa Sallar Janaza,” in ji shi.
Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya da kuma jikoki.