✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Gaza: Netanyahu na neman tayar da Yakin Duniya na Uku

Akinyemi ya ce Netanyahu na neman amfani da rikicin Zirin Gaza ya haɗa Amurka da Iran faɗa

An zargi Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da yunkurin haddasa Yakin Duniya na Uku.

Tohon Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Farfesa Bolaji Akinyemi, ya zargi Netanyahu da nema haddasa yakin duniyar ta hanyar amfani da rikicin Falasdinawa da Isra’ila don hada Amurka da Iran faɗa.

Farfesa Akinyemi ya yi wannan ikirari ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Talata.

Isra’ila babbar ƙawar Amurka na zargin Iran da hannu a harin ba-zatan da ƙungiyar Hamas ta kai mata, inda kungiyar ta kashe akalla mutum 700 ta sace wasu 150.

Iran, wadda ke goyon bayan Hamas ta musanta zargin, a yayin da Faransa ke cewa har yanzu babu hujjar ke tabbatar da hannun Iran a harin na Asabar wanda a kansa ne Isra’ila ta mayar da martani.

An dade dai ana wa juna kallon hadarin kaji tsakanin Iran da Amurka, wadda ta sha jagorantar lafta wa Iran takunkumi.

Ƙasashen duniya dai sun yi ca kan Isra’ila saboda ruwan bamabamai da ta shafe kwanaki hudu tana yi kan Falasɗinawa a Zirin Gaza, inda ta kashe mutum sama da 700 ta rusa gidan mutane kimanin 200,000.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yanke ruwan sha da wutar lantarki hana shigar da abinci da kuma hana shiga da fita da Isra’ila ta yi a Gaza a matsayin haramtacce.

Ko da yake Amurka da Faransa da wasu muƙarrabansu sun nuna goyon baya ga Isra’ilar.

Hukumomin agaji, ciki har da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun jaddada muhimmancin bude Gaza domin isar da abinci da magunguna da sauran bukatun rayuwa a yankin da fiye da rabin al’ummarsa suka dogara da kayayyakin Jinƙai.

A halin da ake ciki kuma, hukumomi a Zirin Gaza sun ce akalla mutum 30 sun mutu sakamakon ruwan bama-bamai da jiragen saman yaki na Isra’ila suka yi a yankin cikin dare.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito kakakin Gwamnatin Zirin na Gaza, Salama Marouf, tana cewa an rusa gidaje da masana’antu da masallatai da shaguna.

Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hare-hare ne a kan wuraren da matakan ƙungiyar Hamas suka ja daga.