Iran ta kakkabo wasu jirage marasa matuka da ake zargin sun kawo mata hari ne daga kasar Isra’ila.
Da talatainin dare ne da aka ji fashewar wasu abubuwan a kusa da filin jirgin birnin Isfahan da ke tsakiyar kasar.
Gidan talabijin na gwamnatin kasar ya ruwaito cewa “an kakkabo jirage uku marasa matuka” a kusa da wani sojoji mai dauke da jiragen yaki samurin F-14 Tomcata a birnin na Isfahan da misalin karfe 12:30 na dare agogon GMT.
Wani kakakin hukumar sararin samaniyan Iran ya shaida wa kafar Aljazeera cewa sun kakkabo jirage marasa matuka, da dama, amma bai yi karin haske ba.
- Taliban ta rufe tashoshin talabijin 2 kan cin zarafin Musulunci
- EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa a jallo
Kafar yada labaran Fars na Iran ta ba da rahoton cewa, gwamnatin kasar ta dakatar da shawagin jirage a kasar sannan ta kunna makamanta na kakkabo jirage da kariyar sararin samaniya.
Amma da daga bisani an dawo da zirga-zirgar jiragen sama yadda aka saba a sasssan kasar .
Ko da yake, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Fars na cewa “Ba a san musabbabin karar fashewar abubuwan da aka ji ba, amma ana ci gaba da gudanar da bincike.”
Shirin Isr’aila
Rahotanni na nuni da cewa ita ma Isra’ila, a nata bangaren, ta kunna makamannta na kariyar sararin samaniya.
Rundunar tsaron Isra’ila ta ce jiniyar gargadin hari sun fara kara a yankunan Arewacin kasar.
Dalilin kai hari Isfahan?
Hari kan cibiyoyin sojin Iran a Syria
Kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA, ya ba da rahoto cewa an kai harin bom kan wasu cibiyoyin sojin Iran da ke a Kudancin kasar Syria.
Rahoto na cewa an kai harehare-haren na Syria ne a filayen jiragen soji da ke Adra da al-Thala da kuma wata rundunar soji da ke birnin Adra da kuma kauyen Qarfa.
Hakazalika an ji karar fashewar abuwa a yankin Al-Imam da ke Babel a kasar Iraq.
Zaman dar-dar tsakanin Iran da Isra’ila
Daga bisa ne Isra’ila ta ce za ta dauki fansa kan harin na Iran, wanda ake ganin shi ne ta kaddamar.
Halin da ake ciki a Isfahan
Kafofin labarai sun ba da labarin cewa al’amaru na gudana lafiya a Isfahan bayan harbo jirage marasa matukan da karar fashewan abubuwa da aka da farko.