✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama shi kan yunƙurin fyaɗe ga ’yar shekara 85

Makwabta sun cafke wani wanda ya yi yunkurin yin fyade ga wata tsohuwa ’yar shekara 85

Makwabta sun cafke wani wanda ya yi yunkurin yin fyade ga wata tsohuwa ’yar shekara 85.

Dubun mutumin mai shekaru 56 ta cika ne a yayin da yake neman zakke wa tsohuwar da karfin tsaya ayankin Uhronigbe da ke jihar Edo.

Tsohuwar ta kai ƙara ofishin ’yan sanda ne bayan makwabta sun kai mata ɗauki a lokacin da mutumin ya kutsa daƙinta ya tube, yana neman keta matuncinta.

Rundunar ’yan sandan jihar ta gabatar da mutumin ga ’yan jarida ne tare da wani matashi dam shekara 29 da ake zargi da yi wa wata ’yar shekara 18 fyade a kauyen Ehor.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, ya ce an kawo karar matashin ne cewa ya yi wa budurwar fyade bayan da ya yaudare ta da sunan zuwa kamun dodon koɗi, ya far mata da ƙarfi ya yi mata fyade.

Jami’in ya ce an kai ta asibiti domin duba lafiyarta.

Ya ce mutum biyun da ake zargi sun amsa laifin amma za a gurfanar da su a kotu.